fidelitybank

Dalilin da ya sa na dawo APC – Sanata Shehu Sani

Date:

Tsohon dan majalisar dattawa mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin da ya sa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bayan ficewa daga jam’iyyar PDP.

Sani ya fice daga jam’iyyar APC ne a watan Oktoban 2018 a yayin da ake ta cece-kuce kan zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Daga nan sai ya sauya sheka zuwa PDP ya samu tikitin takarar sanata na jam’iyyar. Amma ya sha kaye a zaben 2019 a hannun gwamnan jihar Kaduna mai ci Uba Sani.

A ranar 16 ga Fabrairu, Sani ya koma APC tare da wasu ‘yan PDP da ‘yan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party a Kaduna.

Da yake magana a ranar Juma’a a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, Hard Copy, Sani ya ce Gwamnan Kaduna ne ke da alhakin komawar sa jam’iyya mai mulki bayan tattaunawar sulhu a fadin jihar.

Ya ce, “Wani al’amari ne ya sa muka fice daga jam’iyyar APC a wani lokaci a shekarar 2018, kuma lamarin ya sauya, daga nan muka koma APC a jihar Kaduna.

“Da farko ni dan jam’iyyar APC ne, musamman a jihar Kaduna. Mun kafa tsare-tsare, kuma mun yi yakin neman zabe, muka ci zaben 2015 a matakin majalisar dattawa da na gwamna, wani waje kuma muka rabu da gwamna (Nasir El-Rufai) a jihar.

“Mun rabu kan bambance-bambancen da suka shafi siyasa, na kashin kai da ma al’amuran da suka shafi jihar, kuma a dalilin haka ne muka kori kanmu daga jam’iyyar, sannan kuma muka samu sabon gwamna da ya kai mu.

“Gwamnan da yake tuntuba, yana gina gadoji a fadin jihar sannan kuma muka hadu muka amince cewa mu koma jam’iyyar da muka kafa a jihar Kaduna.”

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp