Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa aka cire hoton dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku daga faifan yakin neman zaben jihar.
Gwamna Wike ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jamâiyyar PDP reshen jihar Ribas a ranar Litinin, inda ya yi zargin cewa Atiku ya zabi wadanda yake son yi aiki da su a jihar Ribas ba tare da tuntubar sa ba.
âDan takarar shugaban kasa ya shigo jiha ta ya zabo âyan majalisar shugaban kasa ba tare da gudunmawar gwamna ba. Sun ce ba sa bukatar in yi musu yakin neman zabe.
âBan taba ganin yadda mutane za su raina jiha kamar jihar Ribas su je su zabi makiyan jihar ba, in ba haka ba,â inji shi.
Wike ya kuma yi ikirarin cewa zai yi kamfen ne kawai ga mutanen da suka bukace shi da yin hakan kuma Atiku bai nemi ya yi masa yakin neman zabe ba.


