Kungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama sun fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu, domin matsa ƙaimi ga buƙatunsu na kyautata jin daɗin mambobinsu.
Ma’aikatan sun ce, dole ne hukumomin sufuri na jirgin sama guda huɗu su yi aiki da yarjejeniyar da suka kulla tun a shekara ta 2019 wanda har zuwa yanzu ba a aiwatar ba.
Tun da sanyin safiya ne mambobin ƙungiyar suka tare hanyoyin shiga da fita na dukkan sassan da ke kai wa ga hukumar kula da sufurin jiragen sama.
Lamarin ya janyo cikas ga harkokin sufurin, inda suka cire tutocin ‘yan ƙwadago a sama tare da rera waƙoƙin da suka yi ta zaburar da su domin matsa wa hukumomi lamba, su biya musu buƙatunsu da aka cimma. In ji BBC.
Shugabannin ƙungiyar sun ce yajin aikin na ƙasa baki-ɗaya ne kuma ya shafi kowanne sashe na harkokin jiragen sama a ƙasar.
Harkokin da suka shafi sufurin jiragen sama sun fuskanci tsaiko, inda aka dakatar da ayyukansu, yayin da fasinjoji kuma suka rasa damar shiga filayen jirgi.
An samu cunkoson ababen hawa a kewayen harabar filin jirgin sama na Legas sakamakon toshe hanyoyin shiga da fita.

Da yawa daga cikin fasinjoji da suka shirya tafiya hankalinsu ya tashi wanda ya zama dole suka ɗauki hayar masu babura da aka haramta ayyukansu a jihar, domin kai isa filin jirgin saman, yayin da wasu kuwa suka yi ta tattaki.
Duk wata hanyar shiga tashar jirgin kama daga Ikeja ƘarƘashin gada da titin Agege da Oshodi da kuma hanyar shiga filin jirgin, sun yi cikar kwari da motoci, yayin da ƙungiyoyin ƙwadago suka taru domin yi wa ma’aikata jawabi kan muradunsu.
Cikin bukatun da ƙungiyar ke neman a biya mata, har da abin da ya shafi aiwatar da gyara kan mafi ƙarancin albashi na hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet tun daga 2019.

Rahotanni sun ce wakilan gwamnati kan harkokin sufurin jiragen sama sun kira haɗaɗɗiyar kungiyar domin cimma matsaya tare da dakatar da yajin aikin don kar ya haifar da cikas ga masu tafiye-tafiye.
Sai dai shugabannin ƙungiyoyin sun ce ba za su halarci duk wani zama da wakilan gwamnati ba, face bukatarsu ta biya ba.
Kungiyoyin sun sha alwashin ci gaba da yajin aiki na gargaɗi har zuwa gobe ko kuma lokacin da wakilan hukumomin sufurin jiragen saman suka amince da bukatunsu.