Mai kungiyar Chelsea, Todd Boehly, ya bayyana dalilin da yasa Frank Lampard ya koma kungiyar na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta shafin yanar gizon kungiyar, Boehly ya ce, “Yayin da muke ci gaba da tsayuwa da tsayuwar daka don samun koci na dindindin, muna son samar wa kulob din da magoya bayanmu kyakkyawan tsari da kwanciyar hankali na sauran kakar wasanni.”
“Muna so mu ba kanmu kowace dama ta cin nasara kuma Frank yana da dukkan halaye da muke bukata don fitar da mu zuwa ga Æ™arshe.”
Lampard ya jagoranci atisaye a yau kuma wasansa na farko zai yi da Wolves ranar Asabar.
A mako mai zuwa, Chelsea za ta kara da Real Madrid a wasan farko na gasar cin kofin zakarun Turai ta UEFA Champions League.
An kori Lampard a matsayin kocin Blues a watan Janairun 2021 kuma Thomas Tuchel ya maye gurbinsa.
Sannan Boehly ya kori Tuchel a watan Satumbar 2022 kafin ya kori Graham Potter a ranar Lahadin da ta gabata.