Wata Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano, ta bayar da belin Alhassan Ado Duguwa.
Kakakin kotunan Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce, hakan ya dace da tsarin shari’a, amma za a ci gaba da sauraron shari’ar zargin kisan kai da ake yi masa.
Ya ce Kotun ta kalubalanci rundunar ‘yan sanda saboda kai Alhassan Doguwa gabanta saboda ba ta da hurumin sauraron irin laifin da ake tuhumarsa da shi.
Yan sandan dai na kuma zargin sa da hannu a harbin wasu mutane da bindiga kwana É—aya bayan kammala jefa Æ™uri’a a mazaÉ“arsa ta Doguwa/Tudun wada a zaÉ“en shugaban Æ™asa da na ‘yan majalisar tarayya.
Ana kuma tuhumar ɗan majalisar da laifin kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu guda takwas a ƙaramar hukumar Doguwa a lokacin da ake karɓa tare da bayyana sakamakon zaɓen ɗan majalisar.
Kotun tarayyar ta bayar da belinsa bisa wasu sharuÉ—a ciki har da gabatar da manyan sakatarori biyu waÉ—anda suke aiki a gwamnatin jiha da sarki mai daraja ta É—aya da kuma ajiye fasfo É—in sa a kotun.
Mai shari’a Muhammad Yunusa na babbar kotun tarayyar ya ɗage zaman zuwa ranar 22 ga watan Maris ɗin da muke ciki.
A gobe ne aka tsara komawa gaban kotun majisteret ɗin da ta tura shi zuwa gidan yari, don a saurari shawarar da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano za ta gabatar game da batun.