fidelitybank

Dalilin da ya sa mu ka dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisu – INEC

Date:

Hukumar Zaɓe INEC, ta ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi zuwa mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris.

INEC ta tabbatar da ɗage zaɓen, bayan wani taron gaggawa da manyan jami’an hukumar suka yi a Abuja.

A wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun jami’in yaɗa labarai da wayar da kai na hukumar, Festus Okoye, ta ce, ta ɗauki matakin ne domin samun damar sanya sabbin bayanai a cikin na’urorin BVAS da za a yi amfani da su a zaɓen mai zuwa.

Sanarwar ta ƙara da cewa shari’ar da jam’iyyun siyasa suka shigar a kotu domin samun izinin duba na’urorin da aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasa ne ya kawo jinkiri wurin sauya bayanan da aka yi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasa da wanda ake buƙata domin zaɓen gwamnoni.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan wata kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta amince da buƙatar hukumar zaɓe ta ƙasar ta sake saita na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasar.

Tawagar alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da zaɓen gwamnoni wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris tun da fari.

Hukuncin na nufin kotun ta ƙi amincewa da buƙatar da ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu zaɓen da aka naɗa a zaɓen shugaban ƙasar.

Tawagar alƙalan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na’urar 176,000 da aka yi amfani da su a zaɓen ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ƙin amincewa da wannan shiri ba.

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp