Babban kocin Morocco, Walid Regragui, ya ce, tawagarsa ta doke Brazil da ci 2-1 a wasan sada zumunta na kasa da kasa ranar Asabar, saboda ‘yan wasansa sun nuna tunaninsu a yayin karawar.
Regragui ya kalli yadda Morocco ta doke Brazil a filin wasa na Grand Stade de Tanger, bayan da Sofiane Boufal da Abdelhamid Sabiri suka ci ƙwallayen.
Casemiro ne ya zura kwallo a ragar Brazil a karawar da suka yi da kungiyar Arewacin Afrika.
Da yake magana a taron manema labarai bayan kammala wasan, Regragui ya ce, “Mun so mu yi nasara bayan gasar cin kofin duniya, kuma abin da ya faru ke nan. Mun yi farin ciki domin shi ne karon farko da Morocco ta doke Brazil a tarihi. Suna na farko a cikin jadawalin FIFA.
“Duk da cewa wasu ‘yan wasansu ba sa nan, Brazil har yanzu babbar kungiya ce. Hakanan muna da raunuka, amma mun nuna tunaninmu na ƙwarewa.
“Wannan wata ne na Ramadan, dole ne mu je mu yi sallar Tarawihi don tabbatar da ko gaskiya ne ko a’a. Yanzu za mu yi biki, amma akwai nisa.”
Yanzu Morocco za ta kara da Peru a wasansu na gaba ranar Talata.