fidelitybank

Dalilin da ya sa mahaifina ya yi hayar jirgin ruwa a kan kudi Naira biliyan 2-2 – Florence

Date:

Wata ‘yar gidan attajiri Otedola, kuma furodusa, Florence Otedola, wadda aka fi sani da DJ Cuppy, ta bayyana dalilin da ya sa mahaifinta hamshakin attajirin nan, Femi Otedola ya fantsama miliyoyin fam don yin hayar jirgin ruwa na alfarma don bikin cikarsa shekaru 60 da haihuwa.

A baya-bayan nan ne hamshakin dan kasuwar ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan da aka ce ya fantsama Naira biliyan 2.2, domin yin hayar jirgin ruwan Aristotle Onassis Christina O super luxury da zai yi tafiya na tsawon makonni uku a tekun Bahar Rum.

Yayin da yake kirga bikin zagayowar ranar haihuwarsa, Otedola a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya raba hotuna da dama da ke nuna wasu lokuta tare da danginsa.

Da take magana game da ranar haihuwar mahaifinta akan Instagram, Florence ta raba lokacin jin daɗi tare da sauran membobin dangi a cikin jirgin ruwa na alfarma.

Mawakiyar ta bayyana cewa mahaifinta tun yana karami ya kasance yana mafarkin ziyartar babban jirgin ruwa mai tsayin mita 99 CHRISTINA O domin mallakar abin koyi ne, Aristotle Onassis.

“Don murnar cikarsa shekaru 60, ba wai kawai ya ziyarci jirgin ruwan ba ne, amma ya yi hayar don masoyansa domin mu zauna a nan na tsawon makonni uku masu zuwa. Ina kallon mahaifina, zan iya ganin yadda yake farin ciki, cikawa, kuma har yanzu yana cikin rashin imani. Wannan ita ce yadda soyayya ta kasance, dangi da farko,” ta rubuta.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp