Jam’iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba ta shiga ƙawancen haɗakar ADC shi ne saboda gudun saki-rishe- kama ganye.
Sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar, Injiniya Buba Galadima ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC.
”Su ba su zo suka shiga tamu jam’iyyar ba, sai kawai mu bar tamu mu shiga tasu a wane dalili?”, in ji shi.
Buba Galadima ya ƙalubalnci duka ƴansiyasar Najeriya da kowa ya je ya kafa tasa jam’iyyar ya ga idan zai yi tasiri kamar ubangidansa Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Fitaccen ɗan siyasar ya ce duk da cewa kafa haɗakar zai ƙarfafa adawa a ƙasar amma ya ce haɗakar na da jan aiki a gabanta.