fidelitybank

Dalilin da ya sa kotu ta ƙwace kujerar NNPP ta baiwa APC a Kano

Date:

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha da ke Kano, ta soke zaben Muktar Umar Yerima na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kotun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Yerima tun da farko.

Mai shigar da kara, Hafizu Kawu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kalubalanci bayyana Yerima, yana mai cewa bai cancanta ba.

INEC ta ayyana Yerima a matsayin wanda ya lashe zaben majalisar wakilai na mazabar Tarauni.

Sai dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamitin mutum uku na kotun karkashin mai shari’a I.P. Chima ya ce, Yerima bai cancanta ba saboda ya yi jabun takardar shedar firamare.

Kotun dai ta ce, kariyar da Yerima ya yi na cewa, ya sauya suna a shekarar 2022, kasancewar yana amfani da sunaye guda uku (Umar Mukhtar Zakari) a fasfo dinsa na kasa da kasa tun a shekarar 2009, yayin da takardar shaidar makarantar firamare ke dauke da Umar Mukhtar.

Har ila yau, makarantar firamare da aka ce, makarantar firamare ta Hausawa, ta yi watsi da takardar shaidar da korarren dan majalisar ya bayar.

Don haka aka ce jam’iyyar NNPP ba ta da dan takara a zaben.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp