Fatan dubun dabatar daliban jami’o’i ta kasa ga alama, ya sake dusashewa bayan wata wasikar hukuma ta bayyana cewa gwamnati ta janye umarnin a bude manyan makarantun.
Kungiyar dalibai ta kasa, ta gudanar da jerin zanga-zanga a sassan Najeriya ciki har da rufe harkoki a filin jirgin saman Murtala Mohammed na Lagos, a kokarinta na tilasta janye yajin aikin da malamansu ke yi tsawon watanni.
Gwamnatin dai ta janye umarnin ta na cewa shugabannin jami’o’i su bude manyan makarantun nasu, bayan wani hukunci da kotun ma’aikata ta yi a baya-bayan nan.
A cikin wata wasikar hukuma da aka fitar ranar Litinin, Hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa ta nemi shugabanni da ubannin jami’o’i da majalisun gudanarwarsu su bude jami’o’in gwamnatin tarayya bayan rufe su tsawon watanni saboda yajin aikin kungiyar ASUU.
Sai dai, tun kafin dare ya yi, sai Hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa ta sake fitar da wata wasikar inda ta ce gwamnati ta janye umarnin da ta bai wa shugabannin jami’o’i tun da farko.
Wasikar wadda ta karade shafukan sada zumunta mai dauke da sa hannun daraktan harkokin kudi da asusun ajiyar Hukumar kula da Jami’o’i, Sam Onazi ta ce “An umarce ni, na janye wasikar Hukumar NUC mai lamba: NUC/ES/138/Vol.64/135, ta ranar 23 ga watan Satumban 2022, game da wannan batu na sama”.
Babu dai wani karin bayani kan dalilin da ya sa gwamnati ta yi amai kuma ta lashe abinta game da wannan umarni na bude jami’o’i.