fidelitybank

Dalilin da ya sa ba za mu biya ASUU albashinnsu ba – Gwamnati

Date:

Gwamnatin Tarayya ta faɗi dalilin da ya sa ba ta biya mambobin ƙungiyar ASUU ta malaman jami’a cikakken albashinsu na watan Oktoba ba, tana mai cewa ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su yi ba.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ɗauki matakin daina biyan albashin malaman jami’ar na tsawon lokacin da suka ɗauka suna yajin aiki tun daga 14 ga watan Fabarairu zuwa 14 ga Oktoba.

Bayan dawowarsu aikin ne kuma gwamnati ta biya su albashin kwana 17, kamar yadda ASUU ke faɗa, kuma ta yi barazanar ɗaukar mataki.

Hakan ta sa reshen ƙungiyar na Jami’ar Jos ya umarci malaman jami’ar su yi zamansu a gida, duk da cewa ta ce ba yajin aiki suke yi ba.

Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Ma’aikatar Ƙwadago, Olajide Oshundun, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ba ta yi wa malaman adalci ba.

“An biya su kuɗin aikin da suka yi ne kawai a Oktoba, daga ranar da suka soke yajin aiki,” a cewar sanarwar.

“An ɗauki matakin ne saboda ba zai yiwu a biya su kuɗin aikin da ba su yi ba. Kowa ta kansa yake yi.”

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...

Gwamnati za ta gina titin jirgi a jihohi shida

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da...

Tinubu ya na cikin koshin lafiya – Farouk Adamu Aliyu

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu...

Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar a kamo jagoran ‘yandaban Haiti

Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada...

Gwamnati ta janye karar da ta shigar kan Fasinjar jirgin Ibom

Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan...

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...
X whatsapp