Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya bayyana dalilin da ya sa shi da wasu gwamnonin Arewa suka goyi bayan aniyar shugaban kasa mai jiran gado, Sen. Bola Tinubu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Daura yayin wata ziyarar bankwana da ya kai wa Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar.
A cewar sa, gwamnonin Arewa a karkashin jam’iyyar APC sun goyi bayan Tinubu domin mutunta tsarin jam’iyyar na shiyya-shiyya .
Ya kara da cewa: “Allah ya tseratar da mu daga kunya a zaben da ya gabata a kasar nan inda jam’iyyar mu ta All Progressives Congress APC ta samu gagarumar nasara.
“Duk wanda ke kasar nan mai hangen nesa, to ya sake godewa Allah domin da ace jam’iyyarmu ba ta ci zabe ba, mutane na iya tunanin cewa Gwamnatin Tarayya ta gaza ‘yan Najeriya.
“Duk abin da wani ya shirya a kasar nan, Allah ya taimaki Shugaba Muhammad Buhari ya kare mutuncin sa, domin da a ce mun fadi zabe, da shi ne aka fara zargi.
“Masu hangen nesa sun ga haka, musamman mu gwamnonin da suka fito daga Arewa a karkashin jam’iyyar APC. Mun ga yunkurin bata sunan Buhari.
“Kowa ya san cewa duk jam’iyyun siyasa sun yi imani da tsarin yanki, amma wasu mutane a jam’iyyarmu sun so a ajiye hakan a gefe, amma mun yi watsi da yunkurinsu.”
A cewar Masari, rashin mutunta tsarin shiyya-shiyya da wasu jam’iyyun adawa suka yi ne ya sanya su cikin rigingimun da ke tada su.
“Don haka, da mun yi haka, Allah ne kadai zai san halin da kasar ke ciki a halin yanzu. Saboda haka, dole ne mu ci gaba da cika alkawuranmu.
“Shi ya sa ‘yan Arewa suka yi nasara a lokacin suka kuma samu mutunta mutanenmu, domin da zarar mun ce eh, eh kullum ne,” in ji shi.