Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito an tsige Shaibu a zaman da majalisar ta yi ranar Litinin a Benin, babban birnin Edo.
Tsige Shaibu ya biyo amincewa da wani rahoton kwamitin mutum bakwai da alƙalin alƙalan jihar Daniel Okungbowa ya kafa domin yin bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa mataimakin gwamnan.
A makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar ta Edo ta fara shirin tsige Shaibu. Ƴan majalisa 21 cikin 24 ne suka sa hannu kan takardar ƙorafin.
Sun zargi Shaibu da yin ƙarya da kuma bayyana sirrikan gwamnatin jihar.
A zaman da ta yi ranar Talatar da ta gabata, shugaban majalisar, Blessing Agbebaku ya shaida wa ƴan majalisa cewa wa’adin kwana bakwai da aka bai wa Shaibu ya mayar da martani ga takardar fara shirin tsige shi ya wuce.
Tsige Shaibu na da nasaba da takun saƙar siyasa da ke tsakaninsa da ubangidansa Godwin Obaseki.