Babban layin wutar lantarki na kasa ya sake durkushewa gaba daya da safiyar Litinin, inda ya haddasa daukewar wuta a fadin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan masu amfani da lantarki sun ce sun ga ingantuwar samun lantarki a baya-bayan nan.
Babban layin lantarki na kasa in ji jaridar Daily Trust ya zuwa karfe 10 na safe na samar da megawat 3,712 ga kamfanonin dillancin lantarki kafin layin ya fadi kasa warwas bayan sa’a 1.
Tun cikin watan Yulin bana, masu amfani da lantarki sun ce an samu karin samar da lantarki a bangarori daban-daban.