fidelitybank

Dalilin da ya sa a ka aiyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda — Osinbajo

Date:

 

 

 

 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta aiyana ‘yan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda a hukumance shi ne don baiwa jami’an tsaro damar ɗaukar tsauraran matakai a kansu.

Mataimakin shugaban ƙasan ya baiyana haka ne a fadar Sarkin Katsina a ranar Asabar domin yin ta’aziyya ga Dahiru Barau Mangal, wanda ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Murja.

Osinbajo ya kuma baiyana fatansa na cewa dukkan sabbin matakan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta sun sanya ya kamata a iya ganin sauyi mai ma’ana sosai a harkar tsaron Nijeriya.

Yayin da yake mika godiyarsa ga Sarkin Katsina da sarakunan sa bisa kyakkyawar tarba da aka yi masa, Osinbajo ya yi addu’ar Allah ya ba wa masarautarsa ​​da ƙasa baki daya zaman lafiya.

Ya baiyana ƙwarin gwiwa ce za a samu wadata da farin ciki da kuma zaman lafiya a ƙasar nan kafin wa’adin mulkinsu ya ƙare.

Da yake mayar da martani, Sarkin Katsina, ya bayyana farin cikinsa da ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda a hukumance.

 

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naɗa shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp