fidelitybank

Dalilin da ya sa Ƴansanda ba za su taya EFCC kama Yahaya Bello ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Date:

Kakakin shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya ce jami’an tsaron Najeriya ba su da damar kama tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello saboda ”sarƙaƙiyar” da ke tattare da shari’ar da ake yi masa.

Yayin da yake hira da gidan Talbijin na Channels ta cikin shirin ‘ Inside Sources’ a ranar Lahadi, Mista Onanuga ya ce Yahaya Bello na ɓoye ne a gidan gwamnan jihar Kogi wanda shi kuma kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi kariya.

A watan Afrilun da ya gabata ne hukumar EFCC, mai yaƙi da cin hanci da almundahanar kuɗaɗe ta Najeriya, ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo, saboda zargin laifukan badaƙalar kuɗi da suka kai naira biliyan 80.2

Jami’an hukumar EFCC sun taɓa mamaye gidan Yahaya Bello a yunƙurin kama shi, to amma sai sai aka yi zargin cewa gwamnan jihar wanda ya gaje shi, Usman Ododo ya je gidan domin tseratar da shi zuwa gidansa, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

”To wannan shi ne dalilin” a cewar bayo Onanuga, ”saboda matsalar ita ce idan dai Yahaya Bello na gidan gwamna Ododo, to ‘yansanda ba za su iya kama shi ba, saboda yin hakan ya saɓa wa kariyar da gwamnan ke da ita”.

”Usman Ododo na da kariya, kuma ana ganin Yahaya Bello na ɓoye a gidansa, don haka ‘yansanda ba za su iya zuwa gidan domin kama wani ba”.

”Batun yana da sarƙaƙiya, EFCC a matsayinta na hukumar gwamnatin tarayya, ba za ta iya kama shi ba idan yana cikin gidan gwamnan da yake da kariya daga tuhuma ko kamu”, in Onanuga.

Yahaya Bello ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kogi na tsawon wa’adi biyu.

nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp