Kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya sun janye aniyarsu ta dakatar da aiki a fadin kasar, da suka tsara yi a yau Litinin.
Shugaban kungiyar kamfanonin (AON), Abdulmunaf Sarina, ya bayyana a wata sanarwa ta hadin guiwa da suka sanya wa hannu cewa, sun dauki matakin ne domin gudun jefa tattalin arzikin kasar cikin wani haloi, tare kuma da la’akari da halin tsaro da ake ciki a Najeriyar.
A ranar Juma’a kungiyar ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aikin saboda tashin farashin man jirgi, wato JetA1, inda kamfanonin ke sayen man a kan Naira 700 farashin da kusan ya ninka a wannan shekara, ta wani bangare saboda yakin da Rsaha ke yi a Ukraine, lamarin da ya sa kudin da kamfanonin ke kashewa a harkarsu ya karu da kusan kashi 95 cikin dari.
Gwamnatin tarayya ta roki masu kamfanonin jiragen da su yi la’akari da abin da yajin aikin nasu zai iya haddasawa ga kasar su hakura.