Shahararren mawakin Najeriya, Paul Okoye wanda aka fi sani da Rude Boy a karon farko ya bayyana dalilin rashin jituwar da ke tsakaninsa da dan uwansa Peter wanda ya yi sanadiyar wargaza kungiyar mawakan su ta P-Square.
Bayan shekaru biyar na baraka, Paul Okoye da tagwayensa sun baiwa magoya bayansu mamaki da labarin sulhun su a watan Nuwamba 2021.
Sai dai a wata hira da aka yi da wani mai suna Joey Akan, Paul Okoye a kwanan baya, ya ce rarrabuwar tasu ta samo asali ne daga matsalar iyali kuma ba ta da alaka da waka.
A cewar mawakin, shi da dan uwansa sun yi shiru ba su ce komai ba a lokacin da magoya bayansu ke sukan su ta shafin internet, domin sun san lamarin na da alaka da dangi.