Wani tsohon shugaban matasa na jam’iyyar PDP ya yi hasashen samun nasarar jam’iyyar APC mai mulki a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewar Adeyanju, PDP ba babbar jam’iyyar adawa ba ce.
Makonni biyu kenan da zaben fitar da ‘yan takarar shugaban kasa a babban zaben 2023, ‘yan takara 40 ne suka rage a fafatawar neman tikitin jam’iyyu biyu masu rinjaye a Najeriya.
25 daga cikin ‘yan takarar ne suka gabatar da fom din takarar da suka saya a kan Naira miliyan 100 daga jam’iyyar APC a karshen mika fom din a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wasu daga cikin ’yan takarar da za su yi wa APC tuta a babban taron jam’iyyar na kwanaki biyu a karshen watan Mayu, idan suka samu nasarar tantancewa ba su sauka daga takarar ba, su ne Tunde Bakare; Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade; takwaransa na jihar Ebonyi, Dave Umahi; da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.