Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a jihar sa da kuma Kogi a zaben gwamna, saboda yadda jam’iyyar ta samu karbuwa.
Uzodinma ya dage cewa ‘yan Najeriya na farin ciki da jam’iyyar All Progressives Congress, APC, sakamakon tasirin shugaba Bola Tinubu.
A Imo, Uzodinma ya sake lashe zabensa bayan ya doke abokan takararsa na jam’iyyar PDP da kuma Labour Party.
Dan takarar APC, Usman Ododo shi ma ya yi nasara a jihar Kogi, amma PDP ta yi nasara a jihar Bayelsa inda aka sake zaben Gwamna Douye Diri.
Uzodinma da Ododo sun ziyarci Tinubu a fadar shugaban kasa ta Villa inda suka ba shi takardar shaidar dawowar su.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Uzodinma ya ce nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihohin Kogi da Imo ya nuna “karuwar farin jinin” jam’iyyar.
A cewar Uzodinma: “Kun tuna cewa zaben ranar 11 ga watan Nuwamba, babbar jam’iyyar mu ta APC, na kara samun karbuwa kuma ta fito cikin nasara a jihohin Kogi da Imo.
“Nasarar da muka samu a zaben ya nuna cewa har yanzu ’yan Najeriya na farin ciki da jam’iyyar APC. ‘Yan Najeriya sun kada kuri’a ga shugaban kasa kuma wannan nasara ta tabbatar da wannan ikirarin ta hanyar masu kada kuri’a a jihar Kogi da Imo.
“Don haka mun zo ne domin mu karrama shugaban kasa sannan kuma mu yi amfani da damar mu yi masa godiya bisa goyon bayansa da shawarwarinsa da kuma hikimarsa.
“Ya ba mu damar da kuma nasarorin da ya samu tun lokacin da ya zama shugaban kasa wanda yawancin mu ke amfani da shi don samun damar shawo kan masu jefa kuri’a su zabe mu.”