fidelitybank

Dalilan da ASUU ta sake tsunduma yajin aikin makwanni 8

Date:

Kungiyar malaman jami’o’in ta Najeriya, ASUU, ta sanar da tsawaita wa’adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.

Ya ce makwanni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gaske take kan daukar matakin da ya dace.

ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.

Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.

jalingo news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp