Wani wakili wato daliget na jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya, wanda ya samu kuɗi lokacin zaɓen fitar da gwani, ya raba kudin ga jama’ar karamar hukumarsa ta Sanga da ke Jihar Kaduna.
Mutumin mai suna Tanko Rossi Sabo ya wallafa a shafinsa na Facebook yadda ya raba wa mabuƙata miliyoyin kuɗi bayan ya koma gida.
An yi zargin cewa wasu masu neman takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP sun raba maƙudan kuɗaɗe da suka hada da dalar Amurka ga daliget domin su zaɓe su.
Sai dai jam’iyyar ta PDP ta musanta zargin.
Lamarin ya sa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, ta aike da jami’anta filin zaben fitar da gwanin inda aka gan su suna sanya ido kan abubuwan da ke wakana a dandalin.
Akwai rahotanni daban-daban kan adadin kuɗaɗen da ya samu, inda wasu ke cewa sun kai naira miliyan 12, sai dai hotunan da ya wallafa sun nuna ya raba kusan naira miliyan bakwai. In ji BBC.