fidelitybank

Dalibin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ya rataye kansa

Date:

Wani matashi dan shekara 30 da ya kammala karatun digiri na biyu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Nekede, Owerri, a Jihar Imo, Nerus Elemamba, ya kashe kansa.

An tsinci gawarsa rataye a dakinsa da yammacin ranar Litinin, a kauyensu, a Umuohii, a unguwar Obaoma, a karamar hukumar Ezinihitte-Mbaise ta jihar.

Rahoto na cewa ya rataye kansa nan da nan bayan ya shiga aikin hannu na kauyen wanda ya shafi takwarorinsa.

Wata majiya a kauyen da ta zanta da manema labarai ta ce marigayin bai nuna bacin rai ba kafin ya kashe kansa.

Majiyar ta kara da cewa “Elemamba ya taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan kauye da barkwanci tare da takwarorinsa kamar yadda ya saba.”

“Ba wanda ya san tabbas abin da ya sa shi kashe kansa saboda ya shiga aikin hannu da safe.

Majiyar ta ce “Abin mamaki ne cewa Nerus, wanda ya kasance mai hazaka kuma mai tausayi, zai iya rataye kansa ‘yan sa’o’i kadan bayan aiki,” in ji majiyar.

Ya ce lamarin ya jefa kauyen cikin rudani da fargaba, inda ya ce dole ne a gano musabbabin mutuwarsa kafin a yi jana’izarsa.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Imo, Henry Okoye, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani ba kan lamarin.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp