Dalibin makarantar Kuriga da ‘yan bindiga suka harbe lokacin sace ɗaliban makarantar da ke jihar Kaduna ya rasu.
An kwantar da ɗalibin mai shekara 14 a asibiti ranar Alhamis bayan ‘yan bindiga sun harbe shi.
Maharan ɗake da makamai a kan babura sun yi wa makarantar ƙawanya tare da sace ɗalibai 287, waɗanda shekarun suka kama daga takwas zuwa 15.
Wani malami a makarantar ya ce ɗalibai 25 sun kuɓuta daga hannun maharan alokacin da suke kora su zuwa daji, to sai dai har yanzu sauran daliban na hannunsu.
Mazauna garin Kuriga sun ce lamarin ya shafi kusan duka al’ummar garin.
Wani mutum mai suna Hassan Abdullahi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 17 daga cikin ɗaliban da aka sacen ‘ya’yansa ne.
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a dajin domin tabbatar da kuɓutar da ɗaliban.