Labari da muke samu ya nuna cewa, Allah ya yiwa wani dalibin jami’ar Ahmadu Bello University (ABU), Zaria rasuwa.
Dalibin Bashir Maiwada Zubairu wanda ya kammala karatu kwanan nan, kuma ya fito da sakamakon mafi daraja a cikin daliban da suka kammala a bangaren karatun Injiniya.
A wani wallafa da shafin Instablog9ja ya yi a Instagram, tace, Maiwada ya rasu ne tare da mahaifiyarsa a wani hatsarin mota a ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, a hanyar Kano zuwa Katsina.