Wani dalibin makarantar Sakandire mai suna, Mike Ogbese, ya lakadawa malaminsa mai suna, Ezeugo Joseph, dukan tsiya har lahira a kan ya zane kanwarsa da bulala.
Dalibin Mike wanda ya ke aji na 3 a wata makaranta da ke jihar Delta, lamarin ya faru ne, bayan da ya zargi malamin da lakadawa kanwar sa duka da bulala.
Rikicin ya fara ne a lokacin da aka ce malamin ya yi wa daya daga cikin dalibarsa bulala mai suna Promise, wanda aka ce kanwar dalibin ne.
Ogbeisei ya kasa jurewa bulalar da a ka yi wa ‘yar uwar sa, hakan ne ya yi masa duka, sai ya bi malamin ya yi masa wasu duka wanda daga karshe ya yi sanadiyyar mutuwarsa.