Hukumar jami’ar Obafemi Awolowo da ke jihar Osun, sun tabbatar da mutuwar wani ɗalibi, mai suna Ajibola Ibitayo – wanda ake zargin ya kashe kansa.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar Mista Abiodun Olarenwaju ya fitar ranar Alhamis, ya ce ɗalibin wanda yake aji na biyu – ya kashe kansa ne bayan faɗuwa jarabawa da ya rubuta.
Olarenwaju ya ce an sake sakamakon jarabawar ne ranar Laraba, kuma sakamakon ya nuna cewa ɗalibin zai sake maimaita aji, wanda shi ne karo na biyu da zai yi hakan, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
“Ɗaukacin jami’ar Obafemi Awolowo na cikin alhinin rashin wannan ɗalibi da aka yi,” in ji sanarwar.
Rahotanni sun bayyana cewa ɗalibin ya yi wa kansa allura a gidan mahaifansa bayan ganin sakamakon jarabawarsa.
Shugaban jami’ar Farfesa Simeon Bamire, ya buƙaci iyaye da su riƙa shawartar ƴaƴansu cewa samun koma-baya yayin neman nasara na cikin wani darasi na rayuwa.Dalibi