fidelitybank

Daliban Sokoto dake karatu a Ukraine na cikin firgici – Tambuwal

Date:

Wasu ɗaliban Najeriya ƴan asalin jihar Sokoto da rikicin Rasha ya rutsa da su a Ukraine, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta kwashe su, domin suna ganin daman barin ƙasar zai gagara nan ba da dadewa ba idan lamarin ya tsananta.

Ɗaliban da aka bayyana guda 22 sun yi wannan kiran ne a zantawar da gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya haɗa ta kafar zoom da su tare da kuma iyayensu daga gidan gwamnatin jihar.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta ce, ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna, Aisha Kabir ta shaida wa gwamnan cewa, halin da ake ciki a Kharkiv ya tsananta.

Rahotanni a safiyar Lahadi sun ce, sojojin Rasha sun kutsa Kharkiv, kuma ana gwabza faɗa a birnin na biyu mafi girma a Rasha.

“Muna jin ƙarar harbe-harbe, ko da yake ana ƙoƙarin tafiya da mu cikin bus zuwa Romania, amma direbobin suna jin tsoron za a iya kai masu hari, muna ganin jirgin ƙasa ne ba ya da hatsari wanda za mu yi sauƙin ficewa.” In ji ɗalibar kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Muhammad Bello ya fitar ta bayyana.

Wani ɗalibin kuma Shuaibu Muhammad, ya ce, suna fuskantar ƙalubale a Krakow na Poland domin ba isasshen abinci da wurin bacci mai kyau. “Daga Lviv zuwa Krakow tafiyar awa 12 ce, kuma yawancinmu ba mu san kowa ba da za mu yi magana da shi lokacin da muka iso.

Wasu sun c,e suna fuskantar ƙalubale na yanayin sanyi da rashin tufafin da ya dace da bargon bacci.

Wata ɗaliba Zarah Ibrahimn ta bayyana fargabar cewa “ta ji ana faɗi daga gobe za a hana wa ƴan ƙasashen waje fita Lviv, ta na mai jaddada cewa Kharkiv na tattare da hatsari”

A nasa ɓangaren gwamnan jihar ya yi wa ɗaliban alƙawalin cewa da su da sauran ɗalibai ƴan Najeriya za su fice daga Ukraine nan ba da dadewa ba kuma su dawo gida lafiya.

Gwamnan ya ce ya ba ma’aikatar kuɗi ta jihar umarnin ta tura wa ɗaliban da ke cikin mawuyacin hali tallafin kudi kimanin dala 200 zuwa 300.

Iyayen ɗaliban sun yaba kan yadda gwamnatin Sokoto ta nuna damuwarta da kuma tausayin ƴaƴansu tare da jan hankalin ƴaƴansu da su yi taka-tsan-tsan a yayin ficewa Ukraine. In ji BBC.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp