fidelitybank

Daliban Najeriya sun koka a kan kudin karatun su

Date:

Wasu ɗalibai ƴan Najeriya da ke karatu a ƙasar Birtaniya na kokawa da yadda ɗawainiyar biyan kuɗin karatunsu ta ƙaru sakamakon matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na dunkule tsarin canjin kuɗi da barin kasuwa ta yi halinta.

Ɗaliban sun ce karatu na neman ya gagare su saboda kuɗin karatun ya ƙaru da fiye da kashi 60 cikin ɗari.

Daliban dai masumman ma masu ɗaukar ɗawainiyar kansu sun bayyana cewa suna jin jiki wajen biyan kuɗin karatu ba don jami`o`in Birtaniya sun kara musu kuɗi ba, sai don ddunkule tsarin canjin kuɗi da babban bankin Najeriyar ya yi. In ji BBC.

Matakin dai ya yi sanadin jingine amfani da tsohon farashin gwamnati mai kama da tallafi na naira 471 a kan dala ɗaya, wanda yanzu aka bar kasuwa ta yi halinta.

Lamarin ya jefa ɗaliban cikin kunci da halin kaka-nika-yi kasancewar a halin da ake ciki dala ɗaya ta kai naira 750, yayin da fam ɗaya yake tashi a kan naira 957.

Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sabon tsarin canjin kuɗin, ya sa sai sun yi da kyar da jiɓin goshi suke samun abin da za su yi ciko da shi wajen biyan kuɗin makaranta, hakan ta sa wasu ɗaliban suke rungumar hanyoyi daban-daban na yin kwadago domin su ƙara nauyin lalitarsu abin da kuma ke iya raba musu hankali a karatun da suka je yi.

A watan Yunin wannan shekara ne babban bankin Najeriya ya ɗauki matakin dunkule tsarin canjin kuɗi, inda gwamnati ta yi bankwana da tsarinta na kayyade farashin dala, inda yanzu aka bar kasuwa ta yi halinta.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...
X whatsapp