Ɗalibai ‘yan Najeriya sama da 100 ne ke garkame a gidajen yari daban-daban na Cyprus bayan kama su da hukumomi a kasar suka yi kan zargin sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Shugaban kungiyar ɗalibai ‘yan Najeriya a Turai, Muhammad Bashiru Saidu, ya shaida wa BBC Hausa cewa gwamnatin Najeriya ta yi wa iyaye gargaɗi kan su daina tura yaransu karatu a can.
Gwamnatin Najeriya ta ce an kashe dalibai aƙalla 20 a ‘yan shekarunnan kuma babu wanda aka kama da zargin kisan ya zuwa yanzu.


