Wata ɗaliba ‘yar Najeriya da ke cikin damuwa a Sudan ta shaida wa BBC cewa, wasu ƙawayenta sun maƙale a cikin daji bayan da aka yi kokarin kwashe su, “saboda direbobin bas ɗin sun ce gwamnatin Najeriya ba ta biya su kuɗinsu ba.
Matashiyar mai shekaru 22, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce bas-bas 10 ne kawai daga cikin 14 da hukumomin Najeriya suka yi alkawari suka isa birnin Khartoum a jiya, don haka babu fili da ita da sauran mutane za su shiga.
Har yanzu tana jira a babban birnin Sudan tare da kawarta, kuma tana tsoron gaya wa iyayenta a gida cewa har yanzu babu alamar ƙarin motocin bas.
“Bana son in faɗa musu wannan mummunan labari, mahaifiyata ta shiga damuwa.”
Tana cikin sama da ɗalibai 1,000 da ke ci gaba da fakewa a jami’ar ƙasa da ƙasa ta Afirka da ke birnin Khartoum.
Sun ce suna cikin fargabar cewa za a iya gaya musu su bar harabar nan gaba a yau ba tare da wurin zuwa ba.
BBC ta tuntuɓi tawagar kula da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje domin jin ta bakinsu.