Kungiyar tsofaffin daliban kasar Sudan ta Najeriya, SOSAN, ta yi gargadin cewa sama da daliban Najeriya 2,500 da ba su da takardun karatu sun makale a jami’ar Sudan/African University ba tare da abinci ko ruwa da kudi ba.
Da yake jawabi jim kadan bayan gabatar da addu’o’i na musamman domin kare lafiyar daliban, shugaban kungiyar, Aliyu Abdulkadir Abdulkadir ya ce, sun samu kiraye-kirayen nuna damuwa daga daliban cewa rayuwarsu na cikin hadari matuka.
Ya ce kamar yadda yake a yanzu, hatta dalibai 5,000 da aka ce an kai su Masar har yanzu suna kan iyaka domin ba a ba su izinin shiga kasar ba, yayin da wasu direbobin bas din suka jefa su cikin daji saboda rashin biyan kudadensu.
Abdulkadir ya koka da yadda hatta kudaden da aka ce an ware domin kwashe daliban ana tafka ta’asa, wanda hakan ya sanya daruruwan daliban cikin mawuyacin hali a cikin birnin Khartoum.
Ya ce, “Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa a yanzu haka duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma an ce an yi wa wasu dalibai mata fyade yayin da fadan bindiga ya kai a cikin jami’ar”.
Wani tsohon dalibin jami’ar Sudan Gambo Ado, ya ce har yanzu suna da dalibai a jami’ar Sudan International University of Africa da ke makale. Ya ce yawancin mata ne kuma ba su da abinci ko matsuguni.
Ya ce tuni sun kai rahoto ga gwamnati lamarin daliban da ba su da takardun karatu.
“A yanzu babu wata murya daya da ke magana da daliban Najeriya, kudaden da aka aika musu ba su kai gare su ba, kuma galibinsu sun aika da faifan bidiyo a cikin daji suna ihun neman taimako,” inji shi.