fidelitybank

Daliban Kano 80,000 ne suka samu nasarar cin maki 9 a jarabawar NECO – Kiru

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta ce dalibai 80,000 su ka sami nasarar maki 9 a jarabawar NECO da su ka rubuta a shekarar 2021.

mu nasarar kashi 95 cikin 100 a jarrabawar (NECO) ta shekarar 2021, inda sama da dalibai 80,000 suka samu maki tara.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Alhaji Sanusi Sa’idu-Kiru ne ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai kan nasarorin da ma’aikatar ta samu a shekarar 2021.

Ya ce, “Jihar Kano ce ta fi kowacce yawan dalibai da su ka za na jarrabawar kammala sakandare ta (SSCE) a kasar nan. Mu na da dalibai 89,000, wadanda su ka zana jarabawar NECO a shekarar 2021; daga cikin wannan adadin, kusan 80,000 ne suka samu maki tara, wanda ya nuna cewa mun samu nasarar jarabawar kashi 95 cikin 100 a NECO”.

A cewar kwamishinan, “Gwamnati ta kashe Naira miliyan 235 wajen biyan kudaden jarrabawar wasu daga cikin ‘yan dalibai.

Ya kuma kara da cewar,”Kananan hukumomi 44 da ke jihar, ‘yan majalisar dokokin jihar da na majalisar dokoki ta kasa da kuma masu hannu da shuni, suma sun kashe kimanin Naira miliyan 500 wajen biyan kudaden jarabawar ga dalibai”.

Sa’idu Kiru ya bayyana cewa jihar, ta na da makarantun firamare sama da 7,000 da kuma makarantun sakandire 1,517 a fadin kananan hukumomin jihar 44.

Haka zalika,“ Gwamnati ta kara daraktocin shiyya na manyan makarantun sakandire daga 14 zuwa 23, na SUBEB daga 10 zuwa 15 da kuma hukumar kula da ilimin jama’a daga 10 zuwa 15.

“Ga cibiyoyi masu zaman kansu da na sa kai, bakwai da a ka kafa, hukumar dakin karatu, makarantun kimiyya da fasaha sun samu uku. Domin haka, yanzu muna da ofisoshin shiyya 66 a duk fadin jihar da ke karkashin ma’aikatar MDAs.

“An amince da Naira dubu dari ga kowane shiyya a matsayin kudin gudanar da ayyukan sa ido da kula da makarantun,” in ji shi.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta iya daukar ma’aikata 5,700 da suka cancanci ilimi daga ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomi (MDAs) zuwa aikin koyarwa a aji.

Ya kara da cewa karin malamai 6,995, wadanda ke karbar albashin gwamnati, amma su na koyarwa a makarantu masu zaman kansu da na al’umma an kuma dawo da su koyarwa a makarantun gwamnati a jihar.

Sa’idu Kiru ya ce gwamnati ta kashe miliyoyin Naira wajen siyan litattafai miliyan daya.Gwamnati za ta ci gaba da samar da tsare-tsare da kayayyakin koyarwa a makarantun, domin inganta koyo da koyarwa, hakan zai sa iyaye da dama su tura ‘ya’yansu makarantun gwamnati.

www.leadership ng.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...

Bajintar ɗaliban Najeriya a gasar Turanci ta nuna ingancin ilimi a ƙasa – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya taya ƴanmatan nan uku...

Ƙudirin faɗaɗa mamayar Gaza zai ƙara jefa Falasɗinawa cikin hatsari – MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana rahotannin da ke kwarmata...

APC a Kano mu na jinjinawa Tinubu – Abdullahi Abbas

Shugabannin jam’iyyar APC a jihar Kano, sun yabawa shugaba...

Kwamishinan da ake tuhuma da belin dilan kwayoyi a Kano ya yi murabus

Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi ya...

Turji ya saki Mutane 32 bayan zaman sulhu

Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Bello Turji, ya saki mutane...

ADC ta gargadi El’Rufa’i kan ruguza jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Kaduna,...

An gindayawa Thomas Partey sharudan beli

An gindaya sharuddan belin tsohon dan wasan tsakiya na...

Fursunoni 37 na jiran zartas musu da hukuncin kisa a Bauchi

Fursunoni 37 da aka yanke wa hukuncin kisa bisa...

Kwamitin sulhu na MDD zai gana kan makomar ƴan Isra’ila da ke hannun Hamas

Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai tattauna yau...
X whatsapp