Kimanin dalibai 433 a cikin 836 da suka karantai fannin likitanci a jami’o’in ƙasashen waje sun faɗi jarrabawar samun lasisi da cibiyar yi wa likitoci rijista a Najeriya (MDCN) ta shirya.
An gudanar da jarrabawar ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) tsakanin 22 zuwa 23 ga watan Nuwamban 2023, ta hanyar kwamfuta.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sakamako ya nuna cewa mafi yawan daliban da suka kammala karatun likitancin ba su ci jarrabawar ba.
Dalibai 403 ne kawai suka samu nasara a jarrabawar.


