Akalla matasa miliyan 1.2 ne za su fara cin gajiyar shirin bai wa ɗalibai bashin karatu da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɓullo da shi.
Ana sa ran tsarin shiga cikin shirin, wanda Shugaba Tinubu ya amince da shi a ranar 3 ga Afrilu, zai fara “nan ba da jimawa ba,” kamar yadda Akintunde Sawyer, Manajan Darakta da kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Asusun ba da bashi na Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana.
A ƙarkashin wannan shiri, kashi ɗaya cikin dari na kuɗaden shiga na shekara-shekara na Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS) za ta ɗauki nauyin shirin.
Tare da shirin samun kudin shiga na Naira tiriliyan 19.4 da aka ware wa FIRS a bana, za a iya ware makudan Naira biliyan 194 a matsayin bashin da za a baiwa daliban da suka cancanta.
Sharuɗɗan biyan bashin sun nuna cewa za a fara biyan bashin shekaru biyu bayan kammala aikin yi wa kasa hidima (NYSC).
Sawyer ya zayyana tsarin rajistar, wanda ya nuna cewa wadanda za su ci gajiyar shirin za su bukaci bayar da lambar jarabawarsu ta JAMB, da Lambar Shaida ta Kasa (NIN), da Lambar Tabbatar da Banki (BVN) don neman rancen.
Bugu da ƙari, ɗaliban da suke neman rancen dole ne su ba da cikakkun bayanan karatun su.
“Ga wadanda suka yi nasara samun rancen, za mu biya cikakken adadin kuɗaɗen makarantarsu kai tsaye ga jami’o’in da suke karatu.”
“Haka kuma za a biya daidaikun mutane alawus na amfanin yau da kullum don kula da kansu ta yadda za su iya yin abubuwan.”
“Za su iya amfani da alawus ɗin don tabbatar da cewa akwai isassun dama a gare su don tsira daga wahalar da ɗalibai ke fuskanta.”
Burin Shugaba Tinubu game da shirin ya kunshi kuma yana da nufin fadada hanyoyin ilimi ga ‘yan Najeriya da dama.
Kamar yadda Sawyer ya jaddada, an tsara shirin ne don samun damar shiga da kuma tabbatar da cewa ɗalibai daga sassa daban-daban za su iya cin gajiyar damar samun yin karatu.