Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta tabbatar da cewa dalibai 1,402,490 daga cikin 1,842,464 sun kasa samun maki 200 daga cikin 400, a jarrabawar gamaiyar jami’a ta 2024, UTME.
Hukumar ta fitar da sakamakon ne a ranar Litinin.
Kuma ya nuna cewa adadin da ya kasa samun rabin maki mai yiwuwa kashi 78% na ’yan takara ne.
Da yake karin haske kan sakamakon, magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa, “’yan takara 8,401 sun samu 300 zuwa sama; 77,070 sun samu maki 250 zuwa sama; 439,974 masu maki 200 zuwa sama yayin da 1,402,490 suka ci kasa da 200.”
Oloyede ya kuma ce sakamakon 64,624 daga cikin 1,904,189 da suka zana jarrabawar, hukumar ta hana su kuma za a gudanar da bincike.