Wasu matasa namiji da mace da aka karrama su da lambar zinare a taron wasanni na jami’i’on Najeriya NUGA karo na 26 da aka kammala a jami’ar Legas sun bayyana auren cewa zasu auri junan su.
Kamfanin dillancin labaran kasa (NAN) ya rawaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne wani dalibin jamiāar, Ahmadu Bello Zariya, Sunday Ambule, ya gabatar da bukatar soyayyarsa, Saāadatu Hashime, daga jamiāar daya.
Mataimakin shugaban hukumar ta UNILAG, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe ne ya bayyana haka a ranar Asabar a jawabinsa na rufewa a lokacin da ya kaddamar da soyayya su a dandalin don yabawa mahalarta taron.
Da yake jawabi a yayin taron, Ogundipe ya yabawa daliban biyu bisa kara dankon jin dadin wasannin NUGA na 26.