Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta ce kimanin dalibau 947,000 ne suka zana jarrabawar gama-gari ta shekarar 2023, UTME, a cikin kwanaki biyun da suka gabata.
Kakakin hukumar ta JAMB, Fabian Benjamin ne ya bayyana wannan adadi bayan sanya ido kan jarabawar UTME da ke gudana tare da magatakardar hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede, ranar Alhamis a Abuja.
Da yake jaddada cewa duk wanda ya yi rajista za a ba shi damar rubuta jarrabawar, ya ce JAMB ta warware matsalar fasaha da aka samu a ranar farko ta UTME a wasu cibiyoyi a fadin kasar nan.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Benjamin ya ce 2023 UTME ita ce mafi kyawun jarrabawar da aka gudanar “a cikin wani lokaci.”
A cewar Benjamin: “A cikin kwanaki biyun da suka gabata, ban da yau, mun bincikar ‘yan takara 947,000. Daga cikin ‘yan takara 947,000 mun samu matsala da ‘yan takara kusan 60,000 kuma wadannan ‘yan takarar ana sake jadawalin (na jarrabawar).
“Idan za ku ba da maki, a cikin 900,000, kuna da matsala 60,000, rabo ne mai kyau, amma wannan ba a ce ko dan takara daya ne da bai iya cin jarrabawar ba ba mu damu ba. .”
Fiye da ‘yan takara miliyan 1.5 sun yi rajista don 2023 UTME wanda ya fara a ranar 25 ga Afrilu.