Girgizar ƙasar da ta faru a Morocco ta haifar da labarai masu ta da hankali.
Cikin waɗanda suka mutu har da wasu ‘yan makaranta da babu wanda ya rayu cikinsu.
Wata malama da ake kira Nesreen Abu EIFadel ta yi rashin duka ɗalibanta.
Nesreen Abu EIFadel na Marrakesh – amma Adassel, ƙauyen da dutsen yake nan ne garin ɗalibanta da ita kanta, wanda kuma yana tsaka da inda aka yi wannan girgizar ƙasa.
Wannan malama da ke koyar da Larabci da Faransanci ta koma ƙauyen Adassel inda ta fara lura da yara.
Bayan girgizar ƙasar an sanar da ita cewa duka ɗalibanta 32 da take lura da su da shekarunsu ke tsakanin 6 zuwa 12 sun mutu.


