fidelitybank

Dala na cigaba da cin karanta babu babbaka a Najeriya

Date:

Darajar kuɗin Najeriya naira na ci gaba da durƙushewa yayin da farashin dala ke sake hawa inda a safiyar yau, Juma’a ake sayar da dala daya kan naira 1,360 a kasuwannin canji da ke Abuja, babbar birnin taraya, kamar yadda, Alh Abbdullahi Abubakar, shugaban ƴan canji na Abuja ya shaida wa BBC.

Alhaji Abubakar ya ce tun makon da ya gabata har zuwa yanzu, farashin dala bai sauka ba.

“Tun da aka shiga wannan sabuwar shekarar, farashin dala ke hauhawa, tun ana siyar da dalar kan naira 1,215, a yau Juma’a, farashin dala ta haura zuwa naira 1,360 a kan ko wacce dala kasuwan bayan fage da ke Abuja.”

Abubakar ya ce wasu dalilan da ke haifar da durƙushewar naira kan dala sun haɗa da rashin sa ido daga ɓangaran gwamnati da kuma mutane da dama da ke siyan dalar suna ajiye wa a matsayin kadara.

Ya ce ga dukkan alama, idan har gwanati ba ta tashi tsaye ba, dalar za ta ci gaba da tashi.

A legas kuma, Liman, wani ɗan canji a can ya ce dalar ta tashi itama a kan naira 1,360, a safiyar yau, Juma’a, amma ya ƙara da cewa yanzu da rana dalar ta fara ƙasa inda ta sauka zuwa naira 1355.

Ya ce a jiya Alhamis, an rufe dalar a kan naira 1,349.

A Kano kuma, Yusuf Nabahani, tsohon shugaban kasuwan ƴan canji, shi ma yace kusan kullum farashin dalar ƙaruwa ya ke yi inda ya ce a safiyar yau, Juma’a, dalar ta tashi a kan naira 1,353.

Ya ce a jiya Alhamis, an siyar da dalar kan naira 1,350

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp