Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya ya ce dakarunsa sun yi kaɗan wajen tabbatar da tsaron gaɓar ruwan ƙasar da kuma daƙile satar man fetur.
Da yake magana ta kafar talabijin ta Channels TV a yau Litinin, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ya ce jimillar dakarun rundunar tasa ba su 30,000 da ɗoriya ba.
Sai dai ya ƙara da cewa mahukunta sun ƙara yawan adadin mutanen da suke ɗauka duk shekara domin cike giɓin.
“Za ku sha mamaki idan kuka ji cewa dakarun rundunar sojin ruwa ba su wuce 30,000 da ɗoriya ba,” in ji shi.
“Amma kuma muna da gaɓar ruwa mai girman kashi ɗaya cikin uku na faɗin ƙasar Najeriya baki ɗaya. Muhimmin abu dai shi ne muna ƙoƙarin ƙara yawan dakarun.”