Rahotanni sun ce dakarun bataliya ta 51 na Task Force Banki, Operation Hadin Kai, sun kashe mayakan Boko Haram da dama a Borno.
A cewar Zagazola Makama, wani bugu na yaki da ‘yan tada kayar baya da ya mayar da hankali kan yankin tafkin Chadi, rundunar sojojin tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa ta CJTF ne suka kai samamen a ranar Juma’a.
Jaridar ta ce sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan ta’addar a Gargash, karamar hukumar Bama ta jihar.
Majiyar soji ta rawaito cewa ‘yan ta’addar na shirin kai hare-hare kafin sojojin su kashe su.
An ce an ceto wasu ma’aikatan jin kai biyu da aka sace daga Monguno a shekarar 2022 a yayin fafatawar da aka yi da bindiga.
A halin da ake ciki, akalla mayakan Boko Haram 135 – ciki har da ‘yan uwansu – sun mika wuya ga sojojin birged 21 masu sulke.
Zagazola Makama ya ce wannan ci gaban na daga cikin farmakin da sojojin suka kwashe mako guda ana kai musu a dajin Sambisa tare da hadin gwiwar bataliya ta musamman ta 199 da kuma CJTF.
A yayin farmakin, an ce sojojin sun kori maboyar guda 12, tare da kashe mahara 35.
Yayin da yake jawabi ga rundunar, AE Abubakar, babban kwamandan rundunar (GOC), ya bukace su da su tabbatar da fatattakar ‘yan ta’adda da suka rage da kuma tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin baki daya.