Dakarun RSF da ke yaƙin neman iko da sojojin Sudan sun yi iƙirarin karɓe iko da matatar man fetur ta ƙasar, wadda ke da nisan kilomita 70 daga arewacin birnin Khartoum, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
AFP ya ce RSF sun yi wannan iƙirari ne cikin wani bidiyo wanda ciki suka ce sun kwace iko da tashar lantarki ta Garri.
A ranar Talata, rundunar sojin ƙasar cikin wani bayani da ta wallafa a Facebook ta yi gargaɗin cewa, “wata babbar tawaga mayaka ta nufi matatar, a wani mataki na amfani da damar tsagaita wutar domin ƙwace iko da tashar lantarkin”.