Dakarun tsaron Isra’ila sun ce, za su ci gaba da kai farmaki Gaza da kuma Lebanon.
Sun ce wasu dakaru sun faɗaɗa tare da kai farmaki cikin dare a yankin Jabalia da ke arewacin Gaza.
IDF ɗin ta ci gaba da cewa sojojinta da kuma jiragen sama sun hallaka gomman waɗanda ta kira ƴan ta’adda a hare-haren da suka kai a yankin a cikin kwana guda.
Sanarwar da suka fitar ta ce suna ci gaba da gano maɓoyar ƴan ta’dda tare da lalata maƙamansu a kudancin Lebanon.