Ministan harkokin wajen Mali ya nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwashe sojojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya daga ƙasar ba tare da wani bata lokaci ba.
Abdoulaye Diop a yayin bayanin da ya gabatar a gaban kwamitin tsaro na MDD ya zargi dakarun da zama wani angare na rikicin da asarsa ke fama da shi.
Dakarun wanzar da zaman lafiyar da suka kai su 13,000 a asar sun kwashe shekara 10 a Mali amma sun gaza kawo arshen matsalar da ake fuskanta ta tattsauran ra’ayin addini da rikicin da take haifarwa.
A yanzu sojojin haya na Wagner daga Rasha ne suke taimawa Mali.
Ƙasashen Yamma sun zargi dakarun Wagner da take haƙƙin ɗan adam a Ukraine da wasu yankuna a Afrika, a watan jiya ne kuma MDD ta sanya wa wani babban jami’in Wagner da ke Mali Ivan Maslov takunkumi.


