Babbar kotun tarayya a Abuja,ta ƙi amincewa da buƙatar shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra IPOB da ake tsare da shi, Nnamdi Kanu ta neman a bayar da belinsa, har zuwa lokacin da za a yanke masa hukunci kan laifin cin amanar kasa da gwamnatin tarayya ke tuhumarsa.
Mai Sharia Binta Nyako, ta yi watsi da buƙatar belin tana mai cewa kotu ba za ta bayar da belinsa ba saboda ya taɓa saɓa belin da aka ba shi a 2017. Ta ce kotu na son sanin dalilin da ya sa ya saɓa belin farko kafin har ya sake neman wani.
Kafin zaman kotun a ranar Laraba, Ƙungiyar IPOD da aka haramta a Najeriya ta tilasta dokar zama gida a faɗin yankin kudu maso gabas domin nuna goyon baya ga shugabanta.