An saki Farah Dagogo, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Ribas, kuma dan majalisar wakilai mai ci, bayan shafe kusan wata guda yana tsare.
Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Fatakwal karkashin jagorancin mai shari’a E A. Obile ta yanke hukuncin sakin Dagogo daga gidan yari na Fatakwal a ranar Litinin.
Wannan umarni ya biyo bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci jam’iyyar PDP da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da su gabatar da hujja a ranar 24 ga watan Mayu da ya sa ba za a amince da bukatar da dan majalisar tarayya ya gabatar a kan mutanen biyu da ake kara a zaben fidda gwani na gwamnan jihar.
A bisa umarnin Mai shari’a Obile, an kai Dagogo kotu a keken guragu.
Mai shari’a Obile ya bayar da sammaci ga mahukuntan gidan gyaran hali, inda ya umarce shi (Dagogo) da ya gurfana a gaban kotu kuma a bayar da belinsa bisa ga umarnin da aka bayar.
Sai dai an mayar da Dagogo gidan yari a hanyar Dockyard Road da ke tsohuwar unguwar Fatakwal da jami’an ’yan sanda suka yi, domin kammala duk wasu tsare-tsaren belin da ake sa ran kammalawa nan ba da jimawa ba.
A halin da ake ciki, lauyan Dagogo, Dakta Innocent Ekwu, ya yi barazanar shigar da karar kotu a kan dukkan hukumomi idan aka saba wa umarnin kotun.