Barcelona ta sayi dan wasan gaban Poland Robert Lewandowski daga Bayern Munich, kan kwantiragin shekaru hudu kan Yuro miliyan 50 kwatankwacin Fam miliyan 42.6.
Dan wasan mai shekaru 33 a duniya yana da shekara daya a kwantiraginsa da zakarun Jamus amma a watan Mayu ya ce: “Labari na da Bayern ya kare.”
Ya bi sahun abokan wasansa a Miami a wani bangare na rangadin wasanni hudu da Barcelona za ta yi a Amurka.
Lewandowski ya ce “A karshe ina nan. Na yi farin cikin kasancewa a Barca.”
“Kwanakin baya sun dade sosai, amma an gama yarjejeniyar kuma yanzu zan iya mai da hankali kan sabon babi da kalubale a rayuwata.
“A koyaushe ina son buga wasa a La Liga da kuma manyan kungiyoyi.
“Na zo nan ne domin in taimaka wa Barca ta koma kan gaba da lashe kofuna da dama.”
Lewandowski, wanda ke da yuro miliyan 500 (£425.9m), ya koma Bayern ne a kyauta a shekara ta 2014 bayan ya bar Borussia Dortmund.