fidelitybank

Daga ƙarshe an kori limamin Apo Sheikh Nuru Khalid

Date:

Shugaban kwamitin Masallacin Rukunin Gidajen Yan Majalisa na Apo, Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau, ya ce, sun kori Sheikh Nuru Khalid daga limancin masallacin gaba ɗaya.

Sanata Dansadau ya shaida wa BBC Hausa cewa, sabon matakin ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Khalid din ne a ranar Asabar 2 ga watan Afrilun nan.

A wata wasiƙa da kwamitin masallacin ya fitar a ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun, Sanata Dansadau da aka aike wa Digital Imam, ya ce, an ɗauki matakin korarsa ne gaba ɗaya, saboda ƙin yin nadamar da Sheikh Nuru ya nuna bayan dakatar da shi ɗin.

Wasiƙar ta ce: “Akaramakallah ka fi ni sanin koyarwar Musulunci, manufar ladabtarwa ita ce don a gyara ɗabi’ar mutum.

“Abin takaici, martanin da ka mayar kan dakatarwarka ta nuna cewa, balle ma har ka nuna nadama kan abubuwan da ka faɗa.

“Shugabanci na buƙatar sauke haƙƙi ka’in da na’in. Idan kalamanmu sun ɓata wa ƴan ƙasa rai fiye da faranta musu, to akwai hakki a kanmu na ɗaukar matakin da ya dace saboda al’umma.

“Ga dukkan alamu kuma kamar ba ka da niyyar gyara huɗubarka ta ranar Juma’a ta yadda za ta yi daidai da halin rashin tsaro da ake ciki a Najeriya,” in ji sanarwar.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp